*Typing.....
*JAMILA ƘAZAMA*
( _Sabon Salo_ )
_Labari da /rubutawa_
*Sajida Faɗima*
( _AMARYAR JARUMAI)_
*JARUMAI WRITERS* *ASSOCIATION*
Da sunan AIIah mai rahama_ _mai jin ƙai._
_Yanda na fara rubuta_ _labarinnan lafiya AIIah kasa_ _na gama shi lafiya. ya AIIah_ __ka bani ikon rubuta abinda__ _zai anfani aI'umar musilmi_ _baki ɗaya, inda nan kuskure_ _ubangiji ka yafenin_
*P 1 - 2*
---------------------Shigarsa toilet ke da wuya yaji ya taka wani abu ya zame sai ji kake tum ya zube ƙasa.
"Wash! AIIah na, na karya baya me nataka na zame haka. Abba ya faɗa cikin jin zafin faɗuwar da yai. waige-waige yake ko zaiga abinda ya taka ya zame.
Me idonsa zai gane masa Pampast ne cike da kashi a ka aje a hanya da sauri ya kalli jikinsa, ganin kashi yai caɓa-caɓa a jikinsa har kansa.
"Jamila ! Jamila!! Jamila!!!...
Cikin ɓacin rai yake kiran sunanta.
"Na'am haba dan AIIah kaifa haka kake daga ka dawo zaka fara andabar mutane da kiraye-kiraye na masifa da bala'i wallahi bazaka ta kuramin ba daga dawowarka zaka isheni da kiran tsiya.
Jamila ta faɗa tana nufar hanyar ɗakin Abba.
Ganin bata ganshi a ɗaki ba tasan ya shiga toilet. "jarababbe wankanma yace sai an cuɗashi sai kace wani ƙaramin yaro ni wallahi wannan jarabar ta ka ta isheni ace mutum kullum sai ya yi wanka sau biyu a rana sai kace wani kwaɗo.
Jamila ta faɗa tana nufar toilet ɗin tare da bin ƙofar da harara sai kace ita ta kira ta.
Turus tai ganin Abba a ƙasa ya yi rashe -rashe kamar mai na kuda ya riƙe baya sai faman cije leɓe yake, dariya ta fara harda riƙe ciki kamin ta ce .
"To fa wata sabuwar taɓarance ta tashi na ganka a ƙasa? wai yaro kake so ka dawo ne ban sani ba.......
gani mene ne gaskiya yau bazan samu damar tayaka wanka ba na gaji, baƙi nan nasha aiki nagaji, ya nake jin warin kashi ne ? AIIah yasa dai ba kashi kai mini a ƙasa ba , bazan wanke na 'ya'yan ka ba kuma na wanke naka ai abun sai yai yawa wai shege da hauka.
Jamila ta faɗa tana rife hancinta da hannunta.
Wata tsawa Abba ya daka mata, wacce tasa hantar cikinta kaɗawa.
Take Jamila ta shiga taitayinta.
Tunda ta fara magana Abba yake jifanta da wani mugun kallo, cikin zafin rai da kunar zuciya ya fara magana.
"Wawuya mara hankali da tunani AIIah dai wadare da wannan halin naki na ƙazanta ga mace iya mace amma babu gyara AIIah ya kawo miki sauƙi dole a tayaki da abdu'a AIIah ya yayemiki wannan baƙar ƙazantar taki ace mace sam bata da tsafta ko kaɗan, kullun ɗakinta babu abinda yake sai wari, uban wa ya baki izini ki shigomin toilet? da zaki barmin Pampast ɗin kashi, yanzu sabida AIIah duk toilet ɗin gidan nan bai isheki ba sai kin shigomin nawa sabida tsabar cin mutumci da rashin sanin darajata na san ni bani da mutumci a idonki amma babu komai zanyi maganinki kar ki bari ki kaini bango wallahi idan kika ƙureni abinda zan miki bazaki ji daɗi ba, ƙazamar banza ƙazamar hofi jakar mace wacce babu abinda ta iya sai ƙazanta.
Abba ya faɗa cikin ɓacin rai, tare da jifanta da wani bokiti da ke kusa da shi.
Aguje Jamilata fice daga toilet ɗin, tana gunguni, ma ganganun Abba sun ƙonamata zuciya sosai dan ranta ya ɓaci, amma babu komai zata rama dan ba zai ci banza ba......
"Wallahi duk wanda yaimin kan itace yasin sai na masa na kara ya kwana bai yi barcci ba, ba dai kace mini ƙazama ba zakaga ƙazanta kuwa, wai har ni kake jifa da bokiti kamar wata mahaukaciya AIIah ya isa tsakani na da kai Abba.
Jamila ta ƙarashe maganar da fashewa da wani marayan kuma. haka ta fice daga ɗakin zuciyarta tana saƙa mata abinda za taiwa Abba.
Da ƙar ya rairafa ya dafa bango ya miƙe tsaye.
cikin lokaci ƙalilan ya gyara toilet ɗin yai wanka ya fito, yana wuce, duk abinda Abba yai da kyar ya yi yana yi yana cije leɓe a haka har ya gama.
Kan gado ya kwanta yana maida numfashi, a haka har barcci ɓarawo yai a wan gaba da shi.
Sunturi take a ɗaki kamar mai ɗawafi. ta zauna ta tashi haka taitayi kamar mai basir.
Wayarta ta ɗauko nan da nan tai dalinɗin number ƙawarta Lami, cikin sa'a ringin ɗaya ta ɗaga.
"Hello dan AIIah ki zo yanzu ina san ganinki. daga haka ta kashe wayar, bata jira ansa ba.
Ko minti goma ba ai ba sai Ga Lami, ta shigo gidan kasancewar su basu da nisa makwaftane.
Bakinta ɗauke da sallahma ta shigo ɗakin Jamila.
"To, fa lafiya na ganki a tsaye? kamar me jiran mota, meke faruwa ne kira a fujajin haka wallahi aiki nake haka na a je na zo kiran ki, gani mene ne?. Lami ta faɗa tana ƙarasowa cikin ɗakin.
"Zauna ke dai a kwai matsala sosai a cikin gidan nan, nagaji haƙurina ya ƙare wai kamar ni Abba zai ciwa mutumci haba dan AIIah ai guga ko bai tsiran komai ba yayi na igiya, ina gaya miki ƙawata wallahi yau ɗin nan Abba ya ci zarafi na sosai ya tozartani yamin yamin yamin yamin ɗin tana da yawa.
Jamila ta faɗa tare da fashewa da kuka dan sauran maganar ta cije a bakin ta.
"Uhmmmm AIIah mai iko ai ta tsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, ku ɗai kullum faɗa sai kace kaji haba kufa ba yara bane kun girma yaranku biyu kina ganin duk abinda kuke basa gani suna sane fa kar suke kallan ku, be dace ba gaskiya kidena kulashi kuna raba abin faɗa a gaban 'ya'yan ku koda ya miki ki daurewa zuciyarki kar ki kulashi, ko mahaukaci sai an kulashi ya ke jifa, yanzu dai gaya min me ya haɗaku, kuma ni me zan iya tai maka miki da shi da kika kirani. Lami ta faɗa tana kallon Jamila dan ita take sauraro.
Zama ta gyara ta share hawayan fuskarta, kana ta fara magana a nutse.
"Wai nice ƙazama haka yake cewa kullum bani da tsafta to, ya yakeso nayi da rai na, aiki yamin yawa a cikin gidan nan ga hidimarsa ga ta yaransa tsakani da AIIah da wanne zanji idan na tashin tun safe bana komawa barcci sai dareh, ko lokacin wanka bana samu nayi sabida tsabar aiki ,amma duk da haka Abba baya ganin ƙoƙarina shi a ganinsa ni malalaciyace bana san aiki, daga zaran na gyara gidan nan yara zasu ɓata to, ya akeso nayi da rai na a haka zan ƙare a tsaye ina wallahi ba zai yuhu ba, yau ɗin nan baƙi nan suka cika min gida a cikinsu ban san wacce taje toilet ɗin shi ta cirewa yaranta pampast ba kuma ta barshi a guri bata ɗauke ba. shine ya taka ya zame, sabida AIIah lefenane? da zai ƙare a kai na , bafa ni na cire pampast ɗin ba, da zai ƙare fushinsa a kai na, iya cin mutumci yau dai Abba ya min shi.
Jamila ta kai ayar zance hawaye na zuba daga kwarmin idanuwanta har da shaksheƙa kamar wacce akaiwa tsinan nan duka.
"Tur ƙashi a gaskiya Jamila baki kyauta ba, taya zaki bari wata ta shigar miki ɗakin miji har ta shiga toilet ɗin mijinki ta cirewa ɗanta pampast haba dan AIIah hulaƙancin yayi yawa yasin, ai wannan rashin sanin darajar miji ne, shi ne dan yamiki faɗa kike jin haushi kofa waye akama haka dole yaji haushi tsakani fa da AIIah gaskiya fa ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, ya kamata ki gyara in dai kina san zaman lafiya a gidan aureki, a koda yaushe ina baki shawaran arziƙi, AIIah ya gani dan AIIah dan Annabi, Jamila ki canza ki dawo mace mai tsafta. Lami! ta ƙarashe maganar tare da sauke nainauyar ajiyar zuciya dan lamarin Jamila ya fara isarta.
" Ni zan tafi ina da aiki sosai a gida, naga ina magana kinyi shuru kina kallona kamar abin da na faɗa bai miki daɗi ba ke kin sanni bana tsoran faɗar gaskiya ko a gaban waye a to.
Lami ta faɗa tare da miƙewa tsaye ta nufi hanyar fita.✍🏻
MUje zuwa
*Wannan littafi na kuɗi ne ba* *kyauba duk mai buƙatar* *siya sai yaimin* *magana ta wannan number* *09078373425.*
_Dan AIIah idan baki shirya_ _siya ba karki min_ _magana kar muɓatawa juna_ _lokaci_
*Taku har kullum Amaryar* *Jarumai ce