Tun Ran Gini Tun Ran Zane Hausa Novel

Tun Ran Gini Tun Ran Zane Hausa Novel












TUN RAN GINI

   (RAN ZANE!)

*STORY AND WRITTEN*

*BY*

*MAMAN NOOR*


*TRAILER*

*RELEASE DATE 30th /April /2024


*paid book 300*


*Wannan littafin k'irk'irarren labari *ne, duk wani kama, suna da gari akasi ne*


*TALLA*


Kina ina uwargida ran gida, amarya shalelen mai gida, me kukeyi har yanzu baku mallaki sha yabo sha nema, kayan gyaran jiki mai da tsohuwa yarinya na Maman Meenat wacce tayi fice a fad'in k'asar nan. Shin kinsan da kud'i k'alilan zaki mallaki duk abinda kikeso awajen Maman Maman, kama daga kayan gyara skin irinsu whitening set, lightening set, glow set, milky set, amarya set. wannan saitin idan kika mallake su Hajiya kin wuci sara saidai kiji ana abaki wajen zama awajen taro. 



Kayan Maman Meenat ba anan ya tsaya ba, tanada kayan gyaran da zai maida miki martabarki fiyeda yanda kike tunani, akwai zumar k'iba, hips set, breast set, slimming honey, flat tummy powder hair set, men booster honey, Strechmark oil and cream, hand and foot cleanser kai bari na barku haka, a tak'aice dai duk abinda kike buk'ata zaki samu insha Allahu guarantee ga kyau ga sauk'in kud'i 


Wani abinda dad'in ba sai kin dami kanki da maganar kud'in mota ba, Maman Meenat tanada manyan distributors a different state na k'asar duk garin da kike zaki fad'a sai a had'a ki da distributor garin. 


Me yafi wannan dad'i  nace me yafi shi dad'i y'ar uwa me kike jira har yanzu 

Duk mai buk'atar sanin inda zai sami Maman Meenat akwai social accounts d'inta kamar Facebook @mum meenat organic products 

Ko number ta na whatsapp kamar haka +234 764551049

Maza y'ar uwa nemi naki kafin lokaci ya k'ure miki 


Batasan lokaci ya tafi sosai haka ba, saida taji jabir mai gabatar da labarun k'arfe shida na yamma ya iso ya fara gabatarwa, ta kuma yin hamma ta rufe baki tana korin shed'an da a'uziyya. 


Nusaiba da zuwan ta kenan saboda aikin dare zatayi tace ya dai ASMY naganki har yanzu anan ko dai tayamu kwana zakiyi yau? 


ASMY ta tashi tana gyara wuyan hijabinta tana dad'a kallon d'akin datake kafin ta kuma kallon Nusaiba tace, kar dai har kinzo aiki? 


Nusaiba ta ajiye jakar hannunta a gefe tace bangane har ba, shida fa ta kusa bugawa yanxu haka. ASMY tayi zumbur ta mik'e tsaye tana zazzare manyan idanunta tamkar tayiwa sarki k'arya, sai kuma tace ina NI'IMA take?   NI'IMA? NUSAIBA ta maimaita in a confused way, kafin tace kar dai kice mun ita kike jira? ASMY tace yes ita kai. 


NUSAIBA tayi murmushi tana mai neman wajen zama, kafin tace lallai kece mai zaman jiran gawan shanu, NI'IMAN da tuntuni na had'u da ita zan shiga kasuwa d'azu take ce min zata koma gida saboda bata jin dad'i. 


ASMY ta kuma zaro idanu tace what? yanzu NI'IMA ta koma gida shine ta barni nake jiranta anan yini guda. 


NUSAIBA ta kuma yin dariya ta juyo tace k'ila wani abin kikayi mata tayi fushi yasa tayi deciding ta punishing d'inki ta wannan hanyar. 


ASMY ta d'an yi shiru na dad'i k'u kafin tace nooo! ta nufi table d'inta da d'an gudu ta zaki jakarta tayi waje, tanaji NUSAIBA nayi mata saida safe amma ko juyowa bata iya yi ba ta fita daga harabar wajen ta nufi titi tana addu'ar samun nasarar abin hawa da sauri. 


Cikin ikon Allah kuwa ta samu wani taxi wanda zai shiga dei_dei wanda anan take zama, tayi hamdala tana jin k'aramin relief a tareda ita. har aka iso da ita gida tunanin ta ya tafi can wata duniyar ne. wanda ta tattare shi tas akan NI'IMA datake tsoro da fargaban ko wani abu ne yasameta. 


Don haka addu'a bai bar bakin ta ba, har ta iso gida a yayinda waje yayi duhu sosai tamkar an raba dare, ta nufi k'ofar y'ar k'aramar gidansu tana kallon agogon fatar hannunta daya nuna k'arfe takwas da minti goma daidai. 


Taja gwaron numfashi tana mamakin yanda lokacin ke gudu sosai tamkar ana jansa ne. 


Gidan gidane k'arama ta daidai masu k'aramin k'arfi, wanda kana shiga zaka fahimci hakan, saboda d'aid'aikun d'akin dake gidan wanda bai wuci guda uku zuwa hud'u ba. 


Babu kowa a compound d'in gidan, tasan za'ayi hakan tunda tasan Umma ba hiran dare take yi ba saboda saurin baccinta, NI'IMA dai take sa ran samunta a farke. 


A hankali tayi sallama a k'ofar d'akin kamar mara gaskiya, nayi mamakin ganin d'akin yanada fad'i, don har gado biyu yaci ga kuma y'ar three sitter a ta bakin k'ofa, wanda naga wani yaro a kwance akai. 


ASMY ta kalli gefen datake sa ran ganin Umma anan ilai kuwa harta fara bacci, ta maida idonta kan NI'IMA dake zaune a d'ayan gadon kan cinyarta wani y'ar k'aramar system ne data maida full attention d'inta akansa. 


Suna had'a ido da NI'IMA tayi kicin kicin da fuska, tareda cigaba da abinda take yi. hakan datayi bai dami ASMY ba, jakar hannunta ta ajiye a kusa da wannan yaron ta nufi wajen NI'IMA tareda zama kusa da ita tana murmushi. 


Haba my NI'IMA wai waya tab'a min ke ne sweety? ta k'arashe tana mai tab'o kumatunta datake ta k'ok'arin kumburawa. 


NI'IMA dake k'ok'arin basarwa amma ta kasa, ASMY is one of the people da bazata iya yin dogon fushi dasu ba. 


Kinga ASMY ina yin wani abune mai muhammaci, ASMY ta dad'a k'arfin rumgumar datayi mata tana fad'in, sweetheart har akwai aikin da muhimmancinsa yafi ni. 


NI'IMA ta d'an juyo ta kalleta, ASMY ta kuma langwab'ar da wuya tareda yin fuskar tausayi, NI'IMA ta girgiza kai ta fara k'ok'arin janye hannun ASMY daga jikinta tana fad'in wannan shagwab'ar ko ASLAM yafi k'arfinta, nidai ASMY zanga ranar dazaki yarda kin girmi hakan. 


ASMY tayi dariya tareda sake NI'IMA tana fad'in hoo my NI'IMA waya fad'a miki zan girma a gabanki, kullum ay k'ara zama sweet sixteen nake nothing change. 


NI'IMA ta cigaba da danne dannen datakeyi tana cigaba da cewa, idan kin ga dama ma ki ce yau aka haifeki ASMY, all i knew shine ko ni da kike son tsufarwa kin girmeni, so keep deceiving yourself har sai ASLAM ya shigo miki da surika kya dawo hayyacinki. 


ASMY tayi wani genuine murmushi tana mai kallon gefenta a inda wannan yaron yake kwance yanata faman sharar baccinsa, tsawon mintuna tana kallon shi kafin ta juyo ga NI'IMA da itama ta bar abinda take yi tana kallonta, dukkansu zaka iya ganin tarin emotions acikin idanunsu. 


ASMY ta d'an share guntun k'wallar dake k'ok'arin saukowa daga cikin idonta da yatsa, har yanzu murmushi bai bar fuskarta ba. 


I would love to see yarinyar dazata auri my handsome, honest boy, she would be one of the lucky ones, ko kinsan duk yarinyar datasame shi taji dad'i, ASLAM yaro ne mai hankali banaso yaci karo da sharrin mutane na fili dana b'oye, how i wish i can protect him from the cruelty of this world, ta k'arashe maganar da bitterness a harshenta wanda bai iya b'oyuwa daga k'wayan idonta ba. 


NI'IMA tayi saurin kama hannunta, exactly ASMY! how can you protect him a situation da muke ciki? the world is cruel ba kowa yake da kyakkyawan zuciya kamar naki ba. 


Shiyasa kullum nake baki shawaran hak'ura da wannan stupid show da kikeyi wanda yake janyo attention d'in manyan y'an siyasa akanki, please ASMY you should stop it here NI'IMA ta k'arashe da fuskar tausayi tamkar zatayi kuka. 


ASMY tayi saurin fincike hannunta tareda cewa impossible , ta mik'e tsaye wannan karon ta baiwa NI'IMA baya tareda folding hannayenta ta baya tamkar mai shirin kai naushi. 


Hakan datayi bashi ya hana NI'IMAn cigaba da cewa, ko kiso ko kar kiso zan cigaba da fad'a miki gaskiya wannan hanyar da kika d'auko ba mai b'ullewa bane, wahala kawai zaki sha tareda sanya rayuwar wad'anda kikeso acikin hatsari, please ASMY stop it here! 


ASMY tayi saurin juyowa da fuskarta da ya fara jik'ewa da hawaye, NI'IMA why should i stop? nace ki fad'a min dalilin dazai sa na tsaya bayan hak'ana ta fara cimma ruwa. 


Kina ganin dai abinda ya faru yau NI'IMA, na fara achieving aim d'ina, tayi maganar da tarin emotions d'in dake nuna farin cikin da hakan yasa ta aciki, burina na ganin bayan su ya fara cika, NI'IMA na fara winning. 


NI'IMA tayi murmushi tareda girgiza kai tace what winning are you talking about ASMY ? wannan y'ar k'aramar nasarar da batada maraba da tokan cikin ruwa, kin fi kowa sanin waye sanata gwaram, kinfi kowa sanin mutum ne shi da baya karb'an fad'uwa komai girma da k'ank'antarsa, kinfi kowa sanin zai iya yin komai don ganin ya maido da rashin nasararsa izuwa nasara mai girma ma kuwa. 


Ko kinsan da cewa bake kad'ai ba, hatta ni yanzu nazama cikin wanted list d'insa, wanda a yau d'in nan na kusa fad'awa cikin tarkon daya d'ana, taimakon Allah yasa na tsallake shi. 


Duk da dama nasan aikin danayi miki yau zai samu wannan outcome d'in, amma na yarda nayi miki saboda naga kin jajirce da sai kinyi, and i knew that hakan bazai haifar da d'a mai ido ba, shiyasa i rather risked it naje miki. 


But what scared me the most da har kikaga nayi fushi shine banason wani abu yasamu ASLAM saboda ni dake, am scared that idan suka gano mu they would use our family members to threaten us, most especially ASLAM dayake yaro baisan komai ba. 


ASMY kiyi duba da kyau da nazari, ki tuna dasuwa  kike wannan yak'in, i don't want anything bad to happen to you NI'IMA ta k'arashe tana fashewa da kuka. 


ASMY tayi saurin rumgumeta itama ta fara kukan, aka rasa mai rarrashin wani a cikinsu. 


Subhanallahi! waye ya mutu ni Asabe kuke sharb'an kuka da uwar daren nan, dukkansu sukayi saurin janye jiki suna k'ok'arin basarwa tareda aro murmushi su yafa a saman fuskarsu. 


Umma tayi shiru na y'an sakwanni tana kallonsu d'aya bayan d'aya kamar mai nazarin su, kafin tayi hamma tana fad'in wani abin ne yasameki ASMA'U? ASMY tayi saurin cewa A'a Umma babu komai. 


To kukan naku ta mecece? NI'IMA tayi saurin amsawa, wai fa muna hiran ASLAM ne take kuka wai tana tsoron kar mata su yaudare shi, sai kawai naga ta fashe da kuka. 


ASMY ta zaro idanu tana kallon NI'IMA, kana iya ganin kallon "did you have to tell her this" a fuskarta. 


Umma taja bargo ta kuma kwantawa tana cewa oh to ay sai kuyi ta cigaba da shiriritar ku, ni Asabe zanga yanda d'a zai riga iyayensa aure! 


ASMY ta girgiza kai ta kalli NI'IMA data koma ga abinda take yi tana murmushi, muguwa kinji dad'i yanzu koh? 


NI'IMA ta kuma fad'ad'a murmushin ta tace a little bit. ASMY tace 1:0 amma zan rama. 


Ta d'auki wannan yaron dake kwance wanda nakeyi wa kallon d'an karami but to my surprise zai iya kai shekaru tara zuwa goma. 


D'akin dake gaba dana Umma naga ta bud'e ta shiga, ba laifi shima d'akin yanada girma, saidai bai kai na Umma ba. wani y'ar k'aramar tochi naga ta ciro daga jakarta ta haska d'akin dashi, kafin ta kwantar da ASLAM akan wani katifa. 


Babu gado a d'akin sai wata k'atuwar katifa data cinye rabin d'akin, sai wata rubber chair guda biyu a farkon shiga d'akin, can ta gefe kuma wasu tarkacen kwanuka ne da y'ar k'aramar gas 5kg. ata b'arin katifar kuma wasu akwatuna ne guda uku wanda ba sai an fad'a maka amfaninsu awajen ba. 


Duk da cewa babu wani kaya a d'akin, but it still looks beautiful, very simple and unique. 


Kayan jikinta ta cire ya rage daga ita sai d'aurin k'irji, ta kunna gas d'inta ta d'aura ruwa a wuta. 


Kusa da ASLAM naga ta zauna tareda k'ure shi da idanu hannunta kuwa na yawo asaman kansa yayinda yake cigaba baccinsa cikin kwanciyar hankali. 


Ta share guntun k'wallar dake k'ok'arin saukowa daga cikin idonta da yatsa. 


I would surely protect you, babu abinda zai tab'a faruwa da kai muddin ina raye, kaine farin cikina abinda alfahari na, k'arfin guiwa na, and the only reason that kept me going, ban karaya ada ba, yanzu ma bazan tab'a sarewa ba, bazan ji tsoro ba, saidai su suji tsoro, i would rather let them fear my next move. 


Ta kissing goshinsa, kafin ta rumgumesa, idanunta tuni ya bijire mata ya fara siyaya ruwan hawaye from both eye's, suna sauka saman k'irjin ASLAM da har yanzu take dak'ume dashi. 


NI'IMA ce tayi sallama a hankali tana fad'in Allah sa ba barci kikayi kika manta da cikin ki ba? 


ASMY ta d'ago tana kallon NI'IMA dake rik'e da wata y'ar madaidaiciyar kula a hannunta. bata ce komai ba, kamar yanda itama NI'IMAn bata ce ba harta ajiye mata flask d'in a gefe. 


Har ta juya kamar zata fita sai kuma ta tsaya batareda ta juyo ba tace har yanzu kina sauran lokacinda zakiyi simple life d'in da kikeso dashi, please kar ki bari wani cutarwa tazo wajen yaron da baiji bai gani ba. 


Bata jira jin ta bakin ASMY ba ta fice daga d'akin, ASMY tabi bayanta da kallo tana jin maganar ta NI'IMA ya tsaya mata a wuya sosai harta kasa had'iyar kyakkyawan yawu. 


Tabbas tasan duk abinda NI'IMA ta fad'a gaskiya ne tsagwaronta, duk da cewa tasha fad'a mata hakan bata tab'a yarda ta karyar mata da zuciya ba, akan abinda take son yi ba. but batasan meyasa taji yau tana jin somehow scared ba, k'irjinta tuni yaketa non stop bugu, somehow imagination d'in NI'IMA ne, nothing would happen, abinda ta fara assuring kanta dashi kenan tana k'arawa kanta k'warin guiwa don tasamu ta cika burinta na ganin ta tona asirin miyagun y'an siyasa masu fuska biyu acikin al'umma.  wasu takardu ta ciro daga wani zip na d'aya daga cikin akwatinta 


D'aya bayan d'aya take binsu da kallo tamkar bazata k'ifta, kafin tazo kan wani takarda danaga ta dad'e tana k'are masa kallo. tsawon mintuna tana kallon wannan takardun ba tareda ko k'iftawa ba, kafin tayi wani killer smile tace HONOURABLE SA'AD SANI your day's are numbered! 


***********

HONOURABLE SA'AD SANI DIKKO shine sunan danaji mutane da dama na ambato yayinda sauran comboy d'in motocinsa ke cigaba da ratsa babban titin daya ratsa zuwa ga unguwar maitama, tafiyar ba wata mai tsawo bace ta kawo su ga wata gida da kallo d'aya zakayi masa kasan ta wuci tunanin mai tunani, babu b'ata lokaci moticine suka fara sanya kai cikin wannan rantsastsiyar gida data ci sunanta gida ba muna gida ba. 


Get d'in gidan ma abun kallo ne, wacce take bud'uwa da kanta batareda taimakon mai gadi ba. ko da motar ta faka banga yayi saurin fitowa daga ciki ba, kamar yanda sauran escort d'insa sukayi ba. 


Daga ciki HONOURABLE SA'AD da tuntuni ya lumshe idanunsa tamkar mai bacci har aka iso bai bud'e idanu ba, duk kuwa da cewa yasan sun ison. 


Tsawon mintuna kafin wayarsa daya sakata a one of his misfortune ta kuma yin k'ara, ya yamutsa fuska tareda bud'e idanu a hankali, kamar bazai motsa ba, kafin ya d'an gyara zamansa, gefen ya maida kallonsa tamkar mai tsoron ganin wani abu, har yanzu wayar na suwwar neman agaji, duk kuwa da cewa basai an fad'a maka ta kusa tsinkewa ba. 


Bai d'auka ba kamar yanda nayi tsammanin yin hakan daga gareshi,  hannu naga yasa ajikin farar bluetooth din dake kunnensa na hagu ya dannata. 


Na'am Barrister! ya fad'i a hankali tamkar mai rad'a,  lokaci guda kuma naga yayiwa driver sa sign gesture da hannu, wanda atake ya fice daga motar ya rufe ta. 


Tsawon mintuna da sukayi suna wayar banda uhmm da kad'a kai babu abinda yakeyi, sai daga k'arshe danaji yayi tsaki yana fad'in, did i care? she's no threat to me, don haka kar ka k'ara min maganar wata unprofessional journalist. kit! ya danna wannan bluetoth d'in ya kashe wayar. 


Komawa yayi ya dad'a kishingid'a ajikin kujeran motar tareda lumshe idanunsa a karo na biyu. 


Tsawon minti biyu yana haka, banda hannun shi dake yawo asaman kyakkyawan sajen fuskarsa ba, sai kayi zaton bacci yake a wannan lokacin. 


Kai malam matsa ka bani waje idan ba so kake na talle maka wannan malmalan kan naka mai kamada k'waryan molo ba. ya kuma had'e rai yana muzurai tareda kau da kai tamkar baiji ko A ba a abinda ta gama fad'i ba, hakan da yayi ya kuma tunzurata. 


Dayake masifar take ji wanda yake kama da yanayin halinta, ta kuma hayayyak'o masa tana nuna sa da hannu. kai SHITU kake ko shantu, wallahi zan maka dubun rashin mutunci, har yaushe kayi matsayin dazaka tare ni, the whole me SHAMSIYYA  DIKKO anya kuwa kan ka yana saiti? 


Escort ko kuma ince driver ya kuma k'are mata kallo sama da k'asa, daga ita sai wata y'ar ficilar riga wacce da kad'an ta wuce mata guiwa, ko hannun kirki bata dashi, kanta kuwa ko arzikin d'an kwali babu wanda kallo d'aya zakayi masa kasan yasha alfarman attachment irin curly d'in nan data barbaze shi ba tareda ta kama ba. 


Farachen hannunta kuwa, sun isa amsar da kake nema a matsayin ka na son sanin wacece SHAMSIYYA DIKKO, ko kad'an itada sunanta sun yi hannun riga da kamalarta. 


Ya girgiza kai tareda kauda kai daga kallonta, yana ayyanata  amatsayin mara saiti mai buk'atar agajin gaggawa a psychiatric. 


Izuwa yanzu ta gama kaiwa mak'ura don haka sai cigaba da masifar ta, tareda bangaje sa gefe, hakan ya bata damar isaga jikin motar wanda a yanzu ya bud'e murfin ta, saidai har yanzu bai fito daga ciki ba. 


Without a second thought kamar yanda tasaba ta rumgumesa cikin tsananin farin ciki daya kasa b'oyuwa asaman fuskarta, wanda a ko yaushe idan ta gansa take kasa maintaining d'insa. 


Yayi ajiyar zuciya ba tareda reaction d'in fuskarsa ya canza ba, ya kalli yanda ta tukuikuye kanta ajikinsa, wanda hakan bai masa dad'i ko kad'an, zakayi saurin gane hakan ne daga reaction d'insa. 


Kyakkyawan siraran yatsun hannunsa mai kama dana mata ya sanya akan kafad'arsa inda ta zagaye hannayenta ya janye su a hankali ba tareda yace da ita uffan ba. 


Ta janye jiki itama tana mai yin fuskar tausayi da shagwaba tace, yaya kamar baka murnan ganina ko bakasan yanda nayi missing d'inka bane? kwana biyu kayi mana yaji, gashi idan naje guest house d'inka wad'ancan tirelolin daka ajiye suyi ta zarewa mutum idanu tamkar basu wayeni ba. 


SIYA! ya fad'i a hankali da wata murya mai kama dana gargad'i wanda ba iya muryarsa kad'ai ba, hatta idanuwansa daya saukesu akanta sun bayyana hakan. 


Tayi murmushi mai k'ayatarwa wanda yake k'arawa kyakkyawan fuskarta kyau, ko ba komai wanka ta biya kud'in sabulu, don a rayuwarta babu abinda yake mata dad'i kamar yaya SA'AD ya kirata da SIYA sai taji tamkar batada wani damuwa daya saura acikin duniyar nan. 


Bata jira wani warning d'insa ba ta fice daga motar tana cigaba da murmushin daya kasa barin fuskarta ta nufi ciki, sai kuma ta tsaya ta juyo tana fad'in daddy yace idan ka shigo ka same shi a separate room d'insa. 


Tamkar bada shi tayi maganar ba, duba da irin reaction d'insa a wannan lokacin. wata y'ar k'aramar briefcase ya ciro a k'asan seat d'in kusa dashi ya bud'e ta a nutse kamar yanda yake yin komai cikin nutsuwa. tsawon mintuna yayi yana k'arewa wannan briefcase d'in kallo wanda duk iya k'wak'war ka a wannan lokacin bazaka gano abinda yake yiwa wannan kallon ba. 


Mayar dashi yayi ya rufe ba tareda ya d'au komai ba a ciki ya maida shi mazaunin sa. kafin ya sanya hannu ya rage botiran saman rigarsa guda biyu yana mai sauke gwauron numfashi a jere a jere tamkar wanda numfashin shak'a tayiwa k'aranci. 


Shi kad'ai ya shigo babban haraban parlon gidan wanda daga shi babu irinsa a wannan gidan, ya k'unshi duk wani abun more rayuwar d'an Adam. 


Saidai duk girman shi yana nan very quite tamkar babu mutane aciki, cigaba yayi da tafiya tareda nuna halin ko in kula da yanayin daya tsinci gidan aciki, wanda hakan ke nuna yasaba da hakan. 


Wani corridor yabi wanda ta sada shi ga wasu sashe mai kamada self contained, wanda tun daga nesa ya fara jin hayaniya da muryoyin mutane na tashi sama sama. ya rintse idanu ya bud'e gamida girgiza kai, wanda ba lallai kasan abinda ke cikin zuciyarsa ba a wannan lokacin. 


Haba INNO yanzu fisabillillahi kiji abinda kike fad'a, wai ma wani munafukin ne ya kawo miki wannan k'aryan. 


Eh to lallai SIYAMA! kin girmeni, kin girmi tsufana, yanzu ni zaki kalli idona ki kira da munafuka, mak'aryaciya? abinda uwarki ta turo ki fad'a min kenan? dama nasan HANSAI bazata tab'a yin abin arziki ba tun aurenta har yau alkhairi bai tab'a fitowa daga gareta ba, idan banda naci irin na GAMBO bama mai zaiyi da mummuna fitsararriyar yarinya irinta, gashi duk ta shafa muku muni kun rasa mashinshini. 


SIYAMA da tuni take kunkunbura a tsaye tamkar ana sawa cincin iska, ta juyo tana kallon INNO da wani irin fuska wanda ke fitar da asalin b'acin ran datake ciki. 


Har ta juya zata fita sai kuma ta tsaya ta kuma juyowa tana kallon INNO data bawa banza ajiyarta tamkar ba ita ta gama magana ba, ta maida hankalinta kan wata y'ar k'aramar radio datake ta faman murmurd'awa. 


Kema dai INNO kinsan waye mummuna a gidan nan ba mommy na ba, sannan da kike maganar na rasa mashinshini, kije ki fad'awa wanda baisan YAYA SA'AD ne ya hana kowa zuwa wajena, idan baki sani ba to kisani I'm his one and only love, y'an bakin ciki kuwa saidai su mutu. 


INNO ta ajiye radio, tana kallon SIYAMA kallon k'urilla sama da k'asa har saida SIYAMA ta tsargu itama ta fara bin jikinta da kallo ko akwai wani aibun da INNON ta gani. saidai har yanzu kamar bata gama sanin halin INNO ba. 


Don tuni taji ta fara dariya harda k'yak'yatawa, hakan ya kuma tunzira SIYAMA gamida tsarguwa, kafin taji INNO na cewa ashe dai har yanzu iska na wahalar da mai kayan kara, wai ma wani SA'ADUN kike nufi yanason ki? wani SA'ADUN ne, ko wanda nasani da kullum ake rok'onsa ya aureki amma ya sanya k'afa ya hamb'are yayi fit yace bakiyi masa ba.


Ta kuma murmusawa tareda gyara zama tana fad'in, kyakkyawan fuska dai haka zata tsofe ba'a kai ga gachi ba, kodai mutum ya tsarkake zuciya sai Allah ya taimake shi, ko kuma akai talla masallaci kila asamu wanda zaiyi maneji koba komai yasamu na Subhanallahi! 


SIYAMA ta fashe da kuka tareda juyawa zata fita kenan, shi kuma yana sako kai, suka ci karo a bakin k'ofa. ay kuwa ta rumgume shi tareda fashewa da wani kukan harda na gayya. 


Ya yamutse fuska wanda hakan ke nuna baiso hakan datayi masa ba, hannu yasa a nutse ya janye ta daga jikinshi zuwa gefe, baice mata komai ba, ya cigaba da takowa har inda INNO take zaune wacce tayi lim idanuwanta a lumshe tamkar mai bacci. 


Radio ya fara kashewa kafin ya dawo ya zauna a kujeran dake gefenta, ta bud'e idanu tana fad'in wani d'an banzan ne kuma zai katse min jin dad'i. 


Sai kuma ta kalleshi, oh ay nasan za'a rina, dama dai yau da k'afar hagu na tashi, bansan meyasa mak'iya keson ganin bayana ba. 


Cut the crap! kisa marmin abinda kika dafa yunwa nakeji. 


Wannan karon zama tayi sosai tana kallon shi sai zazzare idanu take, kafin tace sannu  DIKKO! nace sannu DIKKO, kunga dai irin y'ay'an da kuka haifa? laifin me nayi muku da zaku auri matan da basu da tarbiyya, gashi nan y'ay'an ku sun taso ni gaba, daga mai zagina sai mai shirin kai min bugu. 


Duk babu mai tarbiyyar arziki ackinsu, yara dai kamar wad'annan aka samu daga Allah bani. 


Ta kuma kishingid'a tana cigaba da fad'in idan mutum ya isa isashe yayi zuciya yayi aure, ko ba komai yasamu mai wanke masa takashi. 


SIYAMA data biyo bayansa tayi saurin cewa, yawwa INNO na, ay har kashin zan wanke masa indai mukayi aure. 


Don ubaki fice min a d'aki mara kunya mai idanuwan jemage, SIYAMA tayi tsalle wajen k'ok'arin kaucewa jifan da INNO tayi mata saidai duk da haka saida ya sameta a dunduniyar k'afa. 


Ta yamutsa fuska kamar zatayi kuka, don babu abinda SIYAMA ta tsana a rayuwarta kamar abinda zai tab'a lafiyar jikinta. ta durk'usa tareda dafe wajen tana hararan INNO, kafin idonta ya sauka akan SA'AD dake yi mata kallon "kiyi maza ki fice kafin na kai miki nawa bugun" 


Sum sum ta tashi ta fice tana controlling kukanta, wanda tana isa sashensu ta rushe da kuka tana rik'e k'afa, HAJIYA HANSATU mahaifiyarta wacce ke kwance a d'aki kamar ko yaushe, ta taso jiki na rawa jin muryan shalelenta na kuka abinda ta tsana a rayuwarta. 


Kyakkyawa ce itama ba laifi don a kallon farko zaka gano cewa tana alak'a da larabawa ko Shuwa. 


Shalele meya sameki kike kuka kamar an aiko miki da sak'on mutuwa? Hajiya HANSATU ta fad'i with so much care tana rumgumar SHAMSIYA dake dad'a sake jiki tana k'ara muryan kukanta. 


Cikin kukan dake kama dana gayya ta hau bata labarin abinda ya faru harda k'ari, Hajiya HANSATU tayi kwafa yayinda bacin ranta ya fito fili sai kad'a kai take na tsawon mintuna kafin daga bisani tayi saurin kawar da wannan fuskar ta ari wani fuskar tasa wanda hakan yayi matuÆ™ar bani mamaki (A two faced person). 


Haka tayi ta rarrashinta da kalamai masu dad'i, da tarin alk'awarirrika masu dama da zata cika mata. 


**** A b'angaren INNO kuwa SHAMSIYA na fita ta tashi zaune tana kallon SA'AD dayayi k'asa da kai, tareda dafe goshinsa. 


Nan da nan saita d'an saki fuska, ciwon kan ne kuma SA'ADU? ya kad'a kai ba tareda yace komai ba. 


Ta sanya hannu a wata y'ar roban fenti dake gefenta ta ciro wata y'ar container mai murfi ta mik'a masa 


Gashi kaje kayi ta shafawa kana hayak'i dashi, tun satin sama nasa AMIRA ta karb'o shi, nasan wata na k'arewa zaka zo ganin mu ko domin shi. 


Ya karb'i roban yana kallo a hankali kamar mai nazarin wani abu kafin ya sanya shi acikin aljihu. 


Baice komai ba ya mik'e, tayi saurin cewa ina kuma zaka a wannan yanayin? BAFFA TAHIR na nemana, ya bata amsa yana cigaba da tafiya. 


Nan da nan ta hau fad'a, kai SA'ADU dawo ka kwanta, shi TAHIRU baisan shan magani kazo yi ba dazai uzzireka, nasan kuma maganar dai bazai wuci na wannan gafalalliyar y'ar tashi ba. mutane babu tsoron Allah a ransu sai son kai kawai suka iya. 


Kyaleshi kazo kayi kwanciyar ka anan, ni nasan maganin su. 


Bai juyo ba kamar yanda ta umurta ya cigaba da tafiyar sa ba tareda yace komai ba, wanda sai kayi tunanin ko baiji abinda take fad'a bane. 


To ai kaga irinta, dama SA'ADU kai kam ba'ayi maka gwaninta, sai kaje can ku k'arata, girma dai babu hankali. 


Ta koma ta kishingid'a tana cigaba da fad'in kowa yaji dad'in bara baiji dad'in bana ba, Allah jik'anka namiji mazan fama ALHAJI DIKKO......... 


THE UNIQUE PEN WRITER

MAMAN NOOR! 


Paid book 300

Account 8131566709

opay Badiatu Idris Aliyu

Ko katin airtel 0708 949 7392