Andizo Hausa Novel Free Pages

 *ANDIZO*




_Daga alƙalamin_



_*Sarat Alƙasum (Mom Nusy)*_



*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION*



*بسم الله الرحمن الرحيم*



Shafi na 1️⃣

           

           _NIGER  NIAMEY_


Ƙauyen Bangoula. 




Misalin ƙarfe 8:30am na ranar Lahadi, cikin garin Bangoula ya cika da ihu da koke-koken mutanen garin, kowa gudun neman ceto yake suna neman maɓoya, sakamakon harbe-harben da ke tashi ta kowanni lungu da saƙo na ƙauyen, 'yan bindiga sun yi wa garin dirar mikiya. 

Da gudu ta fito da yara huɗu na biye da ita ga tsohon ciki ta yanki daji ko nauyin cikin ba ta saboda tsabar tashin hankalin da suke ciki. Kuka take sosai tana riƙe da hannun yaranta biyu maza biyun na biye da ita duk sun fita haiyacinsu. Suna cikin wannan yanayi sai ga su a wata ruga, hakan ya sa matar ta tsaya tana haki ta dubi yaran cikin wani kalar yanayi ta ce “Umar ku yi sauri ku shiga rugar nan zan biyo ku a baya.” 

Ƙin tafiya suka yi sai da ta ƙara maimaita maganar tana mai ba su umarni tare da nuna musu hanya da hannu sannan suka ruga a guje. 

Durkushewa ta yi a wajen tana salati sakamakon wani azababben ciwo da ya ziyarce ta, ta runƙuya za ta tashi sai ga wata 'yar fulani ta iso gareta, babu ɓata lokaci ta taimaka mata ta tashi ta yo gidansu da ita..

Suna isa gidan jini ya ɓalle mata nan hankalinsu ya yi mugun tashi, su Umar kuka suke suna faɗin “Mamma kar ki tafi ki bar mu.” 

Sun ɗauki fin awa ɗaya tana wannan yanayin tukun ta haifo 'yarta mace santalleliya, murna yaran suke ita kuma a lokacin da kyar take iya gane wa ke kanta. Wata dattijuwa ta amshe jaririyar ta wanke ta itama suka mata wankan. Kallon yarinyar take cike da so da ƙauna tana zubar da hawaye, ta ƙara rungume ta tana jin cikinta na murdawa. 


Wani matashin ɗan fulani ne ya shigo gidan a guje wanda bai fi shekara goma ba yana faɗin “Inna aradu ga su nan mu gudu sun tunkaro gidanmu.” 

Hankalinsu ya tashi duk suka miƙe suna ƙoƙarin guduwa sai jin ƙarar mashinansu suka yi na tunkaro ƙofar gidansu, Inna ta lulluɓe jaririyar ta kalli matar nan ta ce “Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Baiwar Allah tashi mu bi ta baya kafin su shigo.” Ta faɗa tana ruƙo hananyenta. 

Girgiza mata kai ta yi tana kallon yaranta ta ce  “Ku tafi Inna, ga yarana nan don Allah ki kula mini da su, in da hali ku gudu zuwa garinmu ku zauna a can, ni ɗiyar Maigarin garin ce suna na Saude sunan garinmu Tilaberi. Da sun ga Umar za su gane ku don Allah ki mini taimakon nan Inna kar su kashe mini yara, yanzu haka shi mijina ban san a wani hali yake ba, ina kyautata zaton ma sun kashe shi tuni n..”. Ƙarar harbin da suka ji ne ya katse mata magana, ta dinga ruƙon Inna ta tseratar mata da yaranta,hakan ya sa Inna saurin ɗaukan wata butar duma ta miƙa wa wannan yaron nata ya rataya suka bi ƙofar baya wadda take kai su rafin da suke ɗibar ruwa suka dinga gudu.. 


Suna fita su kuma suka ƙaraso gidan, ciki suka kutsa kai inda suka samu Saude kwance tana murƙususu cikin jini, tsawa suka daka mata ɗaya ya saita kanta da bindiga. Da kyar ta ɗago ta kalle su bugun zuciyarta na ƙara yin ƙasa, kafin ta yi magana  take suka harbi ta ko shurawa ba ta yi ba. Haka suka dinga duba ko'ina na gidan ko za su ga wasu amma ba kowa. Ganin ƙofa daga baya suka bi ta nan suna ta kwarara ihu da harbe-harbe, duk wanda suka haɗu da shi take suke kashe shi. Haka suka kashe fiye da rabin fulanin rugar suka kwashe shanu da awakinsu da duk wani abu da suka san zai musu amfani... 


Lokacin su suka fito da  gudu ba su tsaya ba sai da  suka zo rafi, in da suka samu wani ɗan fulani na ɗibar ruwa. A firgice Inna ke sanar masa ya yi maza ya gudu ga abin da yake faruwa, hankali a tashi ya ruga a guje ya nufi gidansa suma suka ci gaba da gudu. Babu abin da kunnuwansu ke juyo musu sai ihun mutane da harbin da ake musu har suka yi nisa sosai da rugar, gindin bishiyar faru mai duhuwa suka tsaya suna mayar da numfashi. Kuka suke marar sauti Inna na cewa su daina kuka kar aje ko sun biyo bayan su, sai da duhun dare ya soma sannan suka tashi suka nausa cikin daji suna ta sauri. Sai da yaran suka dinga faduwa sannan Inna ta ce kawai su samu wani waje su kwanta, cike da tsoro ɗanta Giɗaɗo ya ce “Inna kar fa mu kwanta su biyo bayan mu.” 


“In sha Allahu mun tsare musu mu yi addu'a kawai mu kwanta babu abin da zai same mu. Ka ga jaririyar nan baccin wahala itama take tun kukan da ta yi lokacin da muka zo kusa da rafi.” 

Jiki a sanyaye Ɗahare ta amshi jaririyar ta buɗe buta ta kalli ɗan'uwanta ta ce “Giɗaɗo zubo madarar shanun nan mu gani ko za ta sha  kar ta mutu.” Ta faɗa tana juya ta ta yi luguf kamar ba ta da rai. 

Da sauri ya karkata butar ya zuba mata madarar a hannu, ta dan ɗasa mata a baki, ba ta buɗe bakin ba sai da aka ƙara ɗasa masa tukun ta buɗe baki, cikin jin daɗin Ɗahare ta dinga ba ta har sai da Inna ta ce su barta haka jaiririya ce tukun suka daina ba ta. A daren ranar wannan madarar shanun duk suka sha suka shinfiɗa ɗankwalinsu da zanin da suke ɗaura wa a kugu suka kwanta.. 


Da safe duk suka yi taimama suka yi Sallah sannan suka ci gaba da tafiya, sai da suka kwana suna tafiya in  sun gaji su tsaya su huta da haka har suka samu wani fili mai yashi suka zube a nan sai bacci.. Hasken alfiriji  ya tashe su suka miƙe sai suka gansu a kusa da wani ƙauye, hakan ya sa suka cika da farin ciki nan suka ƙara yin sauri saboda kukan da jaririyar ke tsalawa na yunwa.. 

Suna shiga garin suka haɗu da Limamin garin suka ce masa nan wani gari ne,  ya sanar da su suna cikin garin Tilaberi. Wani daɗi ya ziyarce su suka ce  suna son a kaisu gidan maigarin garin, ganin yadda suke a jigace Liman ya musu jagora suka iso kofar Maigari. Bayan sun gaisa  Maigari ya dinga kallon Umar kamar ya yi magana sai kuma ya yi shuru, Inna na kuka ta mishi bayanin komai tana nuna masa jaririyar da kukan yunwar da take ya sa ko muryarta ba ta fita sai baki da take ɗagawa. Hankalin 'yan fada ya tashi Maigari ya ce a yi maza a kaisu asibiti a duba lafiyar jaririyar su Umar kuma ya kai su wajen maman Saude.


 Mahaifiyar Saude wadda suke kira da Hajja ta rungume su Umar tana kuka, ta sake su ta fito ta bi bayan su Inna asibiti. 


An duba lafiyar jaririyar suka ce yunwa ce kawai ta kusa kashe ta, nan suka nemi a sayo madara a ba ta. Sai da suka yi kwana biyu a asibiti sannan aka sallam su, Maigari na ta kai kawo gabaɗaya damuwa ta hana shi sukoni in ya tuna 'yar sa ma fi soyuwa a ransa. Bayan sun dawo ya ba wa su Inna ɗaki biyu a gidansa aka kewaye musu ya musu komai tare da yi musu godiya, ya tambayi Hajja wani suna suke so a saka wa jaririyar, Hajja ta ce sun ba shi zaɓi duk sunan da ya sa mata daidai ne. Ai kuwa ya saka mata suna Nana Khadija sunan mahaifiyarsa, ya ce amma ana kiran mahaifiyarsa da Hadizuwa.   Giɗaɗo ya rausayar da kai ya ce  “Hai aradu sai muke ce mata Andizo.” 

Ranar su Inna sai godiya suke masa suna kukan farin ciki da suka samu mafaka a wannan ƙauye.. 

 Haka Andizo ta taso cikin so da ƙauna musamman a wajen kakanta Maigari, ba ya son ɓacin ranta ko kaɗan duk abin da take so shi za a mata, hakan ya sa ta sangarce abu kaɗan za ta hau birgima tana kurma ihu sai an rarrashe ta, in ko ba a rarrashe ta ba ranar ba za ta ci abincin gidan Hajja ba tana can wajen Maigari, shi kuma ya yi ta lallaɓa ta har a samu ta sauko ya kawo ta gida..



_BAYAN SHEKARA GOMA_


Andizo yanzu an girma kamanninta da na mahaifiyarta na ƙara fitowa, duka shekarar ta 13 amma wayo kamar ƴar shekara 16, baƙa ce tana da kyau daidai misali, ga ta doguwa sai dai ba ta jiki siririya ce, shi ya sa da ta takalo faɗan da ya fi ƙarfinta sai ta yi saurin  tura ƙawarta Hajaru  a yi damben da ita, in kuwa tafi ƙarfin ka to  ka shiga uku a ƙauyen.. 


Yau aka ke yin sunan haihuwa a dangin su Hajaru, shi ne ta ci biki ta raba wa ƙawayenta goro Andizo ita ce a kan gaba wajen rabon goron bikin. 


'Yanmatan kauyen kowacce ta sha kwalliya an sha foda kamar za su je tashe. Takanas Hajaru ta ja Andizo suka je gidan Liman suka aro akori-kura, Andizo ta shige ciki suka dinga tura ta ƙura na tashi, suna faɗin “Sai kin yi  jikar Hajja.”  


Ita kuwa ta kame a cikin akori-kura ta sha kwalliya kamar fatalwa, bakinta ya sha baƙin kwalli da man leɓe sai maiƙo yake, haka ma samar idanuwanta wani koran janbaki ne ta shafa sai wani far-far take da idanu wai ita ala dole yanga ce take, wuyanta tsakiya ce wata dangajejiya irin ta fulani da suke ɗaurawa a wuya, sai cinko guda biyu a yunwan, hananyenta cike suke da tsakiya kowanni hannu dozin ce, ga ɗan sukuf ɗinta baƙi wani kwafcece ya mata yawa amma saboda tsabar fitina irin na Andizo take sakawa..  Tura ta suke ana ta mata kirari ita kuma tana ci gaba da juya idanu, ji take duk ƙauyen nan babu wadda ta kai ta kyau. 


Wata akori-kura ce ta shayo kwana sai ga su Andizo suma sun shayo kwana ai kuwa ji kake gam!

Wani irin tsalle Andizo ta yi sai ga ta a ƙasa warwas duk suka yo kanta, ta miƙe tsaye tana riƙe bayanta da ya ɗauki zafi ta kalli wanda ya kare su. Shi kuwa tun da suka yi karo ya yi tsaye kamar gunki yana kallon su, Allah ya taimake shi ruwan da ya ɗauko bai zube duka ba jarka ɗaya ce ta tsiyaya. Wani irin ƙanƙance idanu Andizo ta yi tana takowa da kyar saboda ɗan sukuf ɗinta ya cika taf da ƙasa, amma saboda masifa ta rufe mata idanu ba ta ma tsaya ta zazzage ƙasar ba ta iso gaban shi..

Jijjiga jiki ta soma tare da riƙe ƙugu ta lailayo wata gingimemiyar ashar ta sauke mishi tana huci, a fusace ta kuma cewa “Dumadun uban can! waye ubanka a garin nan Ado? Ni za ka yi wa tuffe lule dan mijin babarka? 

In ban ci..”  Tas! Tas!  Marin da ɗaya daga cikin 'yanmatan ta wanka wa Andizo ya hana ta ƙarasa ashar ɗin da ta ɗauko..

Gabaɗaya yaran kowa baki ya buɗe cike da mamakin tsaurin idanun yarinyar, Andizo ta ɗaga kai ta kalle ta wani abu ya zo mata yunwa sai ta yi  baya kamar mai jin tsoro. Ita kuwa yarinyar tana hura hanci ta ce  “Banza ƙazama ke har kin isa ki zagi yayana ban miki ɗaukan amarya na nuna wa Allah na sako ki ƙasa ba.”

Huci Andizo ta dinga yi kamar kasa ta sunkuya da jimƙo ƙasa hannu biyu ta afka mata a idanu, ta dinga tile ta da kasa daga ita har Ado. Da kyar aka janye ta tana ihu tana zagin su, ɗaya daga cikin su  da ta nufi gidan Maigari tun da aka kaɗe Andizo ta dawo tana huci ta ce  “ Maigari yana neman ka a faɗa.”

Cikin Ado ne ya ba da ƙululu! Saboda tsoron da ya ziyarce shi, ita kuwa Andizo ta mimmiƙe ta yi same-same kamar gawa sai wani irin ƙugi take tana bige-bige kamar mai ciwon hauka haka aka nufi ƙofar Maigari....




*_Littafin ANDIZO na kuɗi ne N500. Ku hanzarta ku soma biyan naku kuɗin, ku yi magana da marubuciyar ta wannan number 🥏+966577675904_*




*Taku har kullum Maman Nusaiba ce.*