Zaki Hausa Novel Free Pages

ZAKI


*(Fiery embrace,touch heart memory and a love to remember).*


The story of courage in hero's journey with secret desire”.

          Free page 1


        *Marubuciyar:*

         Walijaam

         The sexy Boss

          Yar tsakar gida

          My Lady boss

          Rainon soja 

          Bafullatanan Ruga

          Siyasata

          Gidan kwarata

          Ƙwarton manya 

          The virgin maid

          Zuma da maɗaci

          Habibi da'iman

          Gidan zaurawa

          Sadaka yalla

          Dijama yar Fulani

          X world duniyar shahara

          Ƴar waye

          Taɓarah

          Yar Aikina

          Ƴar maula

          Ƙwayar sama

 

 


*#Writer*

*#Ayshatou Maman-teddy* 
*Littafin zaki na kudi ne kar a sha'afa ... regular group ₦500 Vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932...idan Vtu transfer ne sai a tura ta Wannan number 09061466409 . Ƴan Niger katin Artel na 500f zaku turo ...Sannan free page ba mai yawa xanyi ba only 5 pages zamuyi na free inshallah


*Bismillahir Rahmanur Raheem


19oct.

1998


Juliana! Juliana!! 

Murya mai cike da amsa kuwa ya katse Ni inda nayi saurin juyawa ina ƙare mawa hajiyar dake tsaye tana sauraren kiran sunan ta da wata murya keyi ta cikin wayar ta , inda ta sanya shi a handsfree . Sanye na ganta cikin shigar Hausawa hannun ta ɗauke da Cazbiha🙀amma ake kiran ta da Juliana!!! . Muryar ta ne ya katse Ni inda naji cike da damuwa ko ina na jikin ta rawa yake yi kar³ kamar mazari. 


Cike da sarƙewar murya ta kira sunan Mahaifiyar nata da Mother”...ya isa! Kar ki kuskura ki ƙara ƙirana da Mother , indai baki amince kin bi umarni na ba komai zai iya faruwa dake da Kuma Wannan Ahalin” . Innalillahi wa'inna ilaihir raji'una...Kalmar da Wacce aka kira da Juliana ta furta kenan wani irin gumi na karyo mata . Cikin zubda Hawaye masu raɗaɗi da kuma zafi ta furta “...No Mother, zan dawo gareku , Amma na roƙe ku ku rabu da Wannan zuri'ar babu ruwan su a komai ”. A yau nake son ganin ki kuma naji labarin bayan Auren ki har Ɗa kin haifa,don haka ki taho dashi ba zamu bari jinin mu ya taso a gurɓace ba , addinin Gaskiya shine Christianity shine addinin gaskiya.....Ba haka bane Mother Christianity addinin wuta ne... Juliana!!! Ta katse ta cikin daka mata Tsawa , tana sarƙewa da Wani irin tari kana cikin raunanniyar murya tace “ Julaina ki kashe Ni kawai ki huta da baƙin cikin da kika dasa mana a zuciya, kika saka maƙiya sukayi mana Dariya . Cikin wata irin dakusasshiyar murya Julaina ta furta “ Zan dawo Mommy, Ina hanya yanzu , zan komo addinin kafurci saboda Ke Mother, duk da nasan wuta ne amma ina roƙon ki ki bar ɗana ya tsira na barshi a dangin mahaifin shi . Ƙittttt!! Taji ta datse kiran. Inda Julaina ta tsaya tana bin Wayar hannun ta da kallo , Kawai sai ta fashe da kuka tana Zubewa a ƙasa tare da cigaba da kukan ta mai ban tausayi . A hankali ta ɗaga Idanunta tana kallon Hoton mijinta ita da yaronta wanda baifi shekaru Uku ba a duniya . Haidar🥹 ta furta sunan tana Zubda Hawaye masu zafi . 


Hannun ta tasa tana dafe ƙirjinta dake buga mata da ƙarfi , Nayi fatan naga yarona Aliyu Ya Rayu cikin Addinin Musulunci amma dole tasa zamu barta badon naso hakan ba , sai dai don nayi biyayya ga mahaifiyata😢 ”. Zan dingi tunani na tsawon Awanni Ashirin da huɗu ta ko wacce rana ba zan taba manta wadanda da Alherin ka gare Ni ba , ta furta tana kafe fuskar hoton mijin nata da kallo . 


Ƙwammm-ƙwaam-ƙwamm...” 


Ƙaran Knocking ya katse ta , inda cikin sauri tasa hannun ta tana goge hawayen dake bin kuncinta . Miƙewa tayi tana nufar ƙofar inda da buɗewan ta tayi ido biyo da Mai kula da Yaron nata gyefe kuma Haidar ne da ganin mahaifiyar nasa ya faɗa jikin ta da sauri itama ta rungume shi , tana jan Ajiyar zuciya tare da saukewa. Laraba Ki shiga masa da school bag ɗin shi , Ni yanzu zan je na dawo zan ɗan fita ’. Okay tom Allah ya kiyaye hanya Hajiya a dawo lafiya”. Yauwa Amin ”. Ta furta tana raɓata tare da rufo ƙofar . Hijab ta saka tana kai hannun ta tare da Ɗaukar wata ƴar akwatin kana ta saɓa yaron dake ta bin ta da kallo , yana ganin baƙon al'amari , don sunan yaro ne amma bai taɓa ganin Mahaifiyar nasa cikin damuwa ba bare yaga hawayenta ...”


Ajiye wayoyin ta tayi

Hannun ta tasa tana saɓa shi tare da ficewa daga Bedroom ɗin nata . 


Rintse ido tayi tana barin ƙayataccen gidan Tana bin sa da kallon ban ƙwana kamin ta nufo inda mai gadin yake tuni ya iso gareta yana faɗin Barka da Warhaka Hajiya Maryam a buɗe Gate ɗin ne?. Hunmm.....Barka Zubairu , A'a zan dan miƙe ƙafa ne yau , ba da moto zan fita ba . To Ranki yadaɗe ya furta yana saurin buɗe mata ƙofan gate ɗin tare da yi mata adawo lafiya....”


Fitan ta ke da wuya ta tadda moton da aka tura mata taxt da zata ganshi a wajen gidan , wannan yasa ta nufar moton baƙa ce ta ko ina bata hango na ciki . Kamin ta ƙarika tuni an bude mata moton tana shigewa suka ja da Wani irin mahaukacin gudu suna barin layin. Juyowa tayi tana bin fuskokinsu da kallo inda a ciki mutum guda ɗaya tak ta sani Wato Madam Silvaline wacce take matsayin yayar Julaina . 


Wani irin kallo take bin Ƙanwar nata dashi , kamin ta fara da cewa “ Kin bamu kunya Julaina , amma ba komai daga yau kinyi banƙwana da Zaman Nigeria ta har abada! Mother tace a sanar dake ko bayan ranta kika dawo bata yafe Miki ba. kuma faɗa mun wani addinin kike ciki yanzu ? Addinin Yesu Almasihu ko....kamin ta ƙare mganan cikin zuba Hawaye Ta furta ina cikin addinin da iyayena suka haife Ni a ciki , Christianity addinin Almasihu . Yashe baki Madam Silvaline tayi kana tace “ Kaji gaskiya wannan itace ƙarshen gaskiya, Waye sunan Yaron ? Ta furta tana kallon kyaƙyƙyawar fuskar baby boy ɗin. Aliyu Haidar! Julaina ta furta a sanyaye , inda cikin cabe baki Madam Silvaline ta furta “ Meye wani Aliyu? Daga Yau sunan sa ALEXANDER😌 . Kasa cewa komai Julaina tayi tana gani Madam Silvaline ta amshi Yaron nata tana masa Wasa tare da cewa “ zaka zauna Dani Alexander? Domin momy a yau zata bar Nigeria sai dai idan ka girma kaje ka ganta a wata rana🙀


Tirƙashi! 

Labari ne mai ban tausayi fiery embrace with a sensual dream soyayya wacce ta kasance ta daban . Kada ki bari wannan tafiyar ayi ta babu ke ehemmm💃🏻😹 .

Taku a koda yaushe #Ayshatou Mamanteddy.#masu buƙatar a tallah ta masu hajar su zasu iya tuntuɓata ta Wannan number 08081202932