Muhimmancin Shan Ruwa A Yini

Muhimmancin Shan Ruwa A Yini




















𝐌𝐀𝐇𝐈𝐌𝐌𝐀𝐍𝐂𝐈𝐍 𝐒𝐇𝐀𝐍 𝐑𝐔𝐖𝐀 𝐀 𝐘𝐈𝐍𝐈





Ruwa ginshikine na rayuwa! A irin wannan lokacin na zafi jiki kan bukacesa koda bakajin kishi, hakika shansa abune da zaisa kaga sauyi a yanayin lafiyarka cikin kankanin lokaci. 

Anso a kalla namiji yasha ruwa kimanin kofi 15, sannan mace anaso tasha kofi 12 akalla. 

Ga wasu daga cikin amfani dagewa shan ruwa musamman a irin wannan lokuta:

■ Yana taimakawa wajen saisaita zafi ajika wato body temperature zatai daidai da yadda mutum zaiji dadin jikinsa

■ Yana nisanta mutum daga kwayoyin cuttukan dake kama kafar numfashi da kuma shiga cikin ciki dake saurin jawoma mutum bukatar karin ruwa Shyasa .

zakuga wani da ya hadu da gudawa ko malaria sai kaji ana sai anqara masa ruwa amma wani ana bashi ORS shikenan... wani ma ko ORS ruwan gishiri da suga basai anbasa ba.

■ Yana gyara fatar mutum, ya hanata bushewa ko tattarewa... harma arika kai ai wance irin matan nan ne da basa tsufa.... 

■ Ga namiji shan wadataccen ruwa na hanaka bubbushewar fata.. zakai kyau ta yadda inka fadi shekarunka ma baza a yarda ba... sai anrika ganin kamar ka ciko da yawa

■ Yana karawa guiwoyin jiki lafiya... da wuya kake fuskantar ciwon guiwa inde ba dama kana dashi ba sakamakon wani ciwo. Toh amma ko kana da ciwon gado irinsu sanyin kashi hakan zai taimakawa guiwoyinka

■ Shan ruwa a wadace na ha66aja aikin kwakwalwa tare da rage nauyi wajen tuna abu da sauri da kuma rashin mantuwa

■ Shan ruwa na maganin ciwon kai musamman wanda keda alaka da stress

■ Shan ruwa na karawa garkuwar jiki karfi wajen yaki da duk wata kwayar cuta da zata kawo ma farmaki... tare da tsaftace jikin daga cutuka.

■ Yana ha66aka lafiyar k'oda wato kidney... ta yadda zata washe tai lafiya taji dadin tace jini tare da saurin datti

■ Shan ruwa na taimakawa koda ta gyara kanta da kanta koda kuwa ta fara samun matsala batare da kasani ba

■ Shan ruwa na taimakawa wajen metabolism wato narkar da abinci da hana cushewar ciki

■ Shan ruwa na saisaitawa tare da rage kiba wato obesity ko overweight 

■ Yana taimakawa wajen saisaita karfin tafiyar jini ajika wato blood pressure da kuma larurar sugar

■ Yana goge fata ta yadda wani ko bai shafa mai ba zakaga fatarsa shar take

■ Yana magance matsalar tsakuwa acikin koda wato kidney stonez tare da tsaftace mafitsara daga kwayoyin cuta saboda yawan fitsarin da mutum zai keyi
 
■ Shan ruwa na taimakawa wajen saurin tofowar gashi wato asami tsawon gashin kai tare da walkiyarshi.

■ Yana hana saurin fashewar jiki koda an karcesa da wani karfe...

■ Yana hana ciwon mara musamman ga mata yayin haila... yawan shan ruwa kan sassauta hakan.